An Gudu Ba’a Tsira Ba

Austrian fire fighters move flower pots as they clean mud from the columbarium at the cemetery in the Austrian-German border town of Schaerding, along the flooded river Inn June 5, 2013. Torrential rain in the south and south-east of Germany caused heavy

A jihar Indiyana, wani mutum dake gudun kamun ‘yan sanda ya shiga cikin bangon gidansa don ‘buya, ya kuma makale har na kwana ‘daya saida ‘yan aikin kwanakwana suka cece shi.

Mutumin mai suna Steven Shuler a kokarin sa na gujewa ‘yan sanda lokacin da suke nemansa, kan laifin ‘kin bin umarnin alkali na hukuncin jeka gyara halinka da aka yanke masa, hakan ya kai shi ga shiga cikin wani ‘dan rami cinkin bangon gidansa dake kusa da murhun ‘dumama gida.

Shugaban ‘yan kwana-kwana yace, Steven ya makale cikin katangar har sama da kwana guda saboda bazai iya fita ba, wani abokinsa da ya kawo masa ziyara ne ya sameshi cikin wannan hali yakuma kira ma’aikatan ‘yan kwana-kwana domin neman ceto.

Bayan ceto shi da duba lafiyar sa, ‘yan sandan dai sun kame shi zuwa gidan yari.