A yayin da ake cigaba da kokarin kawar da cutar polio mai nakasa kananan yara daga Najeriya kwata kwata, inda nan ne da kasashen pakistan da afganistan da indiya har yanzu ake samun cutar a duniya.
An shiyya ma 'yan jarida taron bita a jihar Naija, domin jaddada muhimmancin rawar da sukan taka a matsayinsu na 'yan kishin kasa wajan yakar wannan cutar da ta gallabi kananan yara, Mohammed Ibrahim babban jami'i ne a shirin ya kuma kaddamar da kasida a taron
Wasu daga cikin 'yan jaridar da suka halaci wannan taro dai sun bayyana farin cikin su musamman ta yadda ake kokarin kawar da cutar daga doron kasa gabaki daya kuma sunyi alwashin fadakar da al'uma dangane da illolin cutar da kuma hanyoyin da za'a bi da zasu taimaka domin ganin kawo karshen cutar.
Daga karshe masana sun yi karin bayanin cewar sabon maganin wanda yanayin bada shi ya banbanta da wanda ake digawa yara a baki wani gagarumin cigaba ne kuma yana da tasiri kwarai.