Jiya Litinin ne ‘yan sandan Birtaniya suka bayyana cewar suna neman wasu ‘barayi da suka shiga wani gida suka kuma sace mesa har guda talatin da takwas.
Su dai wadannan macizai da aka sace basu da dafi, kuma sun hada da mata masu ciki guda takwas, an sace sune daga wani gida inda ‘yan sandan sukace an ga wasu mutane biyu suna barin gidan rike da buhunhuna biyu.
Jami’in ‘yan sandan garin Merseyside, Neil Henry yace, “wadannan tarin macizai dai an dade ana tara su”
Bisa ga wani shafin yanar gizo na masu rainon mesa, yace macizan suna girma kuma tsayinsu na kaiwa kafa hudu zuwa biyar, kuma ana amfani dasu a matsayin dabbobin gida, suna da halayya mai kyau da saukin juyawa.
Jami’an ‘yan sandan dai sunce, yana da matukar wuya macizan su zama barazana ga al’umma.