An Sake Bude Asibitin Kayyade Iyali Da Zubar Da Ciki Wanda Aka Kaiwa Hari

Yanzu haka an bude asibiti nan mallakar cibiyar nan mai fadakarwa da yekuwar kayyade iyali, a jihar Colarado dake a Amurka, bayan ta kwashe watanni uku a kulle.

Kulle wannan Asibitin dai ya biyo bayan wani harin da wasu mahara suka kai a asibitin ne inda suka kashe mutane uku kana wasu tara suka ji rauni.

Ko a yanzu haka kofar shiga Asibitin yana nan a lalace, domin lokacin da ‘yan sanda suka yi kokarin hana maharan kai harin ne aka lalata kofar.

Vicki Cowart shugaban kungiyar tace ko a jiya Littini sai da Asibitin ya karbi majinyatan gaggawa da yawan su yakai 30.

Tace asibitin zaici gaba da aiki sosai cikin dan kankanin lokaci ciki ko har da zubar da ciki.

Sai dai ko a jiyan saida masu zanga-zangar nuna kyamar su ga zubar da ciki suka gudanar da wata zanga-zanga akan titin da asibitin yake, sai dai kuma masu zanga-zangar sun nisanta kansu da harin da aka kai a asibitin inda suka bayyana tausayin su ga wadanda suka samu rauni sakamakon wannan harin