Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mata Da Kayan Kamshi


'Yan mata da dama kan yi amfani da kayan shafe shafe dangin su turare masu kamshi harma lamarin ya zamarwa wasu tamkar sunyi gado ne tun kaka da kakanni.

A cewar 'yan mata da dama, anfani da kayan kamshi musamman turare wajibi ne ga kowace diya mace domin kuwa a cewar su, mata 'yan kwalliya ne musamman na wannan zamani da muke ciki.

Idan mai karatu bai manta ba, jiya mun zanta da wasu samari akan yadda samari kan yi amfani da turare kuma sun bayyana mana irin nasu tunanin harma wasu daga ciki suka nuna cewar bai zama dole ba a wurin su domin a cewar su, mata aka sani da kwalliya.

Daya daga cikin 'yan matan da suka bayyan mana ra'ayoyin su ta ce wasu samarin ko sun mai suka shafa sai jikin su yai wari, inda ta kara da cewa mhusamman lokacin zafi.

Saurari cikakkiyar hirar a Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG