Wani bincike akan shayar da jarirai mama ya nuna cewa akwai bukatar a akara azama wajen yin fadakarwa da kirkiro shirye-shiryen da za su taimaka akan shayarwa a kasashen da suka cigaba da masu tasowa.
Binciken mai suna Lancet Breastfeeding Series ya gano cewa za ‘a iya magance mace-macen yara 820,000 a duk shekara ta hanyar yin fadakarwa akan shayarwa. Bugu da kari, binciken ya gano cewa za a iya magance mace-macen mata sanadiyyar cutar dajin nono kusan 20,000 a duk shakara idan aka sami Karin masu shayarwa.
Shirin ya kuma ya gano cewa rashin shayar da yara mama na janyowa yara jinkiri wajen koyo da fahimtar abubuwa da ma magana.
Wani likita mai suna Nigel Rollins mai aiki a fannin haihuwa, da na kula da jarirai da matasa na Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO), ya fadi cewa tsawon lokaci da kuma yawan lokutan da uwa ta shayar a cikin shekarun da ta ke haihuwa, na rage hadarin kamuwa da cutar dajin (cancer) nono da kusan kashi 6. Haka kuma ya na rage hadarin kamuwa da cutar dajin mahaifa.
Wani babban kalubale shine yadda masu yin madarar jarirai ke jan hankalin mutane wajen yin amfani da madarar, abinda kuma ke kawo cikas ga shayarwa wadda ta fi muhimmanci a farkon rayuwar dan'adam.
Dr. Rollins ya kuma ce daya daga cikin hanyoyin da za su dace a bi wajen magance wannan kalubalen shine, hukumar kiwon lafiya ta sa ido akan kamfanonin da ke yin madarar.