An Tsokano Kudar Zuma A Gyadigyadi Kano

Rahotanni daga jahar Kano sun bayyana cewar da misalin karfe goma sha daya na safiyar yau ne a daidai randabawul din gyadi gyadi kusa da gadar Alhaji Ado Bayero, wata annoba ta tashi wadda ta yi sanadiyyar kai wasu ga asibiti.

Kamar yadda wasu ganau suka bayyana, wasu ma'aikatan wuta ne wato NEPA suka tsokalo wani gidan zuma a yayin da suke kokarin daukar ani tsohon tsani da suka aje da dadewa.

Kudan zuman ya mamaye dukkan wurin inda shaidun suka bayyana cewa jama'a da dama sun yarda abubuwan hawan su domin gudun neman tsira, wasu mata da ke dauke da kanannan yara kuma sun bar yaran sun gudu. Lamarin ya shafi duk masu tallar da ke kusa da wurin inda ake lodin mota domin kuwa jama'a sun farfasa masu kayan sana'a a kokarin tserewa harbin zuman.

Jama'ar wurin sun bayyana cewar sai da matasa suka yi kukan kura suka dauko tsofaffin tayoyi suka banka masu wuta sa'annan hayakin ya sa kudan zuman ya koma cikin kogon sa.

A yanzu haka dai rahotannin sun bayyana cewa an sallami mutane biyu daga cikin wadanda kudan zuman ya harba daga asibiti, kuma kawo yanzu komi na tafiya dai dai kamar yadda aka saba.