Rahotanni da dama sun bayyana yadda wani firij ya kusa hallaka mutane goma sha daya dan tsananin warin sa a wata jami'a da ke Kentucky.
An kai mutanen asibiti ne cikin gaggawa ranar larabar da gabata, bayan warin da suka shaka daga wani firij da ke aje a sashen binciken kananan halittu da ke a jami'ar. Shidai firij din ana anfani da shi ne wajan ajiyar wasu sinadaran da ake anfani da su wajan aikin binciken.
Manyan hukumomin jami'ar sun bayyana cewar an canza wa firij din wuri ne ranar talata, inda aka dauko shi daga wani sashen bincike a jami'ar zuwa wannan ginin domin anfani da shi wurin binciken kimiyya.
Babban jami'in 'yan kwana kwana Joe Best ya bayyana cewar mutanen da aka kai asibitin na karbar magani domin warin ya harbi wasu sassan fatar jikin mutanen da idanun su, kuma suna fama da matsalar jiri.
Mai magana da yawun jami'ar Kathy Jones ta bayyana cewar wani sinadarin da aka yi anfani da shi wajan wani bincike ne ya haifar da warin. A yanzu haka dai an fitar da firij din daga harabar makarantar, an kuma ci gaba da aiki da daukar karatu ranar larabar da abin ya afku da yamma kamar yadda aka saba.