WASHINGTON, DC —
An yi ta jin kararrakin ruwan bama-bamai da harbe-harbe yau jumma'a a cikin dazuzzukan dake kusa da garin Chibok a Jihar Borno, yayin da sojoji na Najeriya da masu ba su shawara ke ci gaba da shirye-shiryen kwato 'yan mata dalibai da 'yan Boko Haram suka sace.
Mazauna garin na Chibok sun ce tun daga misalin karfe 9 na safiyar yau jumma'a, sun yi ta jin fashewar bama-bamai a yayin da jiragen saman yaki suke shawagi a samaniyar garin da kuma dazuzzukan da suke kusa, musamman ta wani yankin da tun farko aka ce nan aka fara tsayawa da dalibai mata da aka sace daga wannan garin.
Haka kuma mutanen garin na Chibok sun musanta rahotannin dake cewa an tsallake bakin iyaka da 'ya'yansu zuwa makwabta, su na masu cewa sun yi imanin har yanzu su na cikin wannan daji na Sambisa.
Ga bayani daga bakin wani mazaunin garin na Chibok.

Your browser doesn’t support HTML5