Ana Karfafa Zaton Cutar Ebola Ta Yadu Zuwa Mali - 4/4/2014

Jami’ai a Mali su na binciken wasu mutane uku da akle karfafa zaton sun kamu ne da cutar Ebola, a daidai lokacin da ake samun bullar annobar wannan cuta a yankin Afirka ta Yamma.

Yau jumma’a ministan kiwon lafiya na Mali, Ousmane Kone, ya bada sanarwar wadannan mutane uku.

Ma’aikatan kiwon lafiya sun aike da jinin mutanen uku domin ayi gwajinsu a wani dakin binciken kimiyya na nan Amurka a birnin Atlanta. A halin da ake ciki dai, an kebe wadannan mutane daga sauran marasa lafiya ana yi musu jinya dabam.

Hukumar kiwon lafiya ta Duniya ta ce mutane akalla 86 sun mutu daga cutar Ebola a kasar Guinea Conakry, tare da wasu mutanen su 7 a makwabciyarta Liberiya.

Hukumar ta ce tana binciken wasu mutane 154 da aka tabbatar ko ake zaton sun kamu da wannan cuta ce a yankin Afirka ta Yamma, akasarinsu a kasar Guinea.

Wannan shi ne karon farko da aka samu bullar annobar Ebola a Afirka ta Yamma. A can baya, cutar ta fi bulla a kasashen yankin tsakiyar Afirka