Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa tayi babban kamu daga kungiyar Manchester City, bayan da ta karbo shi aro, amma yanzu ya sa hannu domin ya yiwa Aston Villa wasa har na tsawon shekaru hudu.
Dan shekaru ashirin da shida da haifuwa Scott Sinclair, ya farfado da bajintansa a faggen wasan kwallon kafa tun da ya je kungiyar Aston Villa, a watan Janairu wannan shekarar, inda ya ci masu kwallaye uku kuma ya kasance ana sashi kusa kowane wasa.
Koda yake ba’a bayyana adadin kudi da aka biya ba, bayan da aka bayyana komawarsa Aston Villa a jiya talata, yace farin cikinsa baya iya misaltuwa .
Sinclair, dai ya bugawa Ingila wasan kwallon kafa a gasar Olympic na shekarar 2012, kuma Manchester City ta sayen shine daga Swansea City, akan tsabar kudi dala miliyan 9 da dubu 600.