Duk da cewa ilimin mata na cike da kalubale, ana samun cigaba yanzu haka don wasu kam basu bari a bar su a baya ba.
Wata mata mai suna Malama Zahra Miko Yakasai ta koma makarantar sakandare aji uku don kammala karatunta duk da cewa tana da aure da 'ya'ya.
Malama Zahra dai ta fadi cewa ta bar makaranta ne lokacin da take aji uku a sakandare, tayi aure, amma albarkacin mijin da ta aura wanda dan boko ne ya sa ta fara karance-karance. Da taimakon Allah bayan kamar shekaru 14 sai ta samu ta koma makarantar sakandare har ta kammala.
Malama Zahra bata tsaya nan ba, ta yi sha’awar shiga jami’a don karanta aikin jarida kuma ta rubuta jarabawar da ake kira JAMB a turance amma bata sami adadin makin da ake bukata ba. Sai ta je ta yi digiri a Hausa, ta kuma dora da diflomar a aikin jarida.
Babu dai wani babban kalubale da Malama Zahra ta fuskanta sai ma karin karfin gwiwa da ta samu . Ta kuma yi kira ga mata da su maida hanakali wajen neman ilimi don shekaru basa hana boko.