A tattaunawar da shirin samartaka yayi da wasu matasa samari da ‘yan mata akan auren zumunci, sun bayyana mana ra’ayoyin su.
A take ne matasa?
Hirar ta fara ne da wata matashiya waddad ta bayyana nata ra’ayin inda ta ce, “auren zumunci na da matukar dadi musamman idan ma’auratan sun yarda da juna, domin kuwa tamkar ‘yan gida daya ne tunda jinni guda ne. saidai mtsalar it ace idan aka sami matsala, to takan bata zumuncin iyalan baki daya.”
Sai kuma matashi mai suna Jamilu Haruna, wanda ya bayyana nasa ra’ayin inda yace a matsayin sa na matashi, abinda kawai zai sa ya yarda da auren zumunci shine idan shi ya ga yariyar da kansa kuma suka amince da juna, to shine kawai zai iya sa shi ya yarda a yi masa auren zumunci. A mma bazai taba yarda iyaye ko wasu ‘yan uwa su saka shi cikin matsala ba.
Tambaya anan itace! Idan ta kasance matashi ya nuna ra’ayin sa kan budurwa kuma ta kasance suna da dangantaka, iyayenta baza su takura mata ta auri dan uwan nata ba?.
Matashin ya bayyana cewar koda kuwa iyayenta sun tursasa mata, da zarar sun fara zance zai iya ganewa saboda ko yadda zata saki jiki ta yi Magana da shi daban ne musamman idan akwai soyayya tsakanin su.
Saurari cikakkiyar hirar.