Babban Sakataren MDD Ya Bayyana Damuwa Kan Daliban Chibok - 8/5/2014

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya bayyana matukar damuwa game da makomar dalibai mata da aka sace a Chibok a Jihar Borno. Mr. Ban Ki-moon ya bayyana jimaminsa ga iyalan wadannan ‘yan mata da kuma al’ummar Najeriya baki daya.

Babban sakataren na MDD ya jaddada cewa kai farmaki a kan yara kanana ko makarantu, babban laifi ne karkashin dokoki na kasa da kasa, kuma babu wata hujja a duniyar nan ta aikata shi.

Sakatare janar din yace yana bin sawun wannan al’amari sosai, ya kuma sake jaddada kudurin MDD na goyon bayan Najeriya wajen takalar wannan.

Babban sakataren ya kuma buga waya ma shugaba Goodluck Jonathan domin jajanta masa.