Barcelona Zata Kece Raini Da Juventus A Gasar (UCL) 2016/17 Quarter Final

A jiya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta yi waje rod da takwararta ta Bayern Munich, ta kasar Jamus, da ci 4-2 a bangaren gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai Uefa champion league, na shekarar 2016/2017 a matakin wasan kusa da na kusa da na karshe (Quarter final) a karawarsu ta biyu.

A haduwarsu ta farko Real Madrid, ta yi tattaki har zuwa Jamus ta doke Bayern Munich, da kwallaye 2-1 wannan nasara da Real Madrid, ta samu a jiya ta bata damar hayewa zuwa zagaye na gaba Semi final, da kwallaye 6-3

Ita ma Atletico Madrid, tayi waje da Leicester City, bayan sun tashi kunnen doki a wasan da suka yi a jiya a kasar Ingila, A satin da ya wuce ne Atletico ta doke Leicester, da ci daya mai ban haushi a kasar Spain don haka Atletico, ta samu nasarar kaiwa ga zagaye na gaba (Semi final) a gasar ta (UCL) ta bana

A yau kuma za'a cigaba da sauran karashen wasannin Inda kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, zata kara da Juventus,sai Monaco, ta karbi bakuncin Borussia Dortmund, ta kasar Jamus. Za'a fafata wasanninne da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar, kamaru da kasar Chadi.

Your browser doesn’t support HTML5

Barcelona Zata Kece Raini Da Juventus A Gasar (UCL) 2016/17 Quarter Final