Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Barje Gumi Tsakanin Bayern Munich Da Real Madrid


A cigaba da fafatawa da akeyi a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) na shekara 2016/2017 a matakin wasan kusa da na kusa da na karshe Quater final jiya kungiyar kwallon kafa ta Juventus, ta lallasa takwararta Barcelona, dake Spain da kwallaye 3-0 a karawarsu ta farko.

Juventus ta samu nasarar jefa kwallonta ta fari ne a cikin minti bakwai da fara wasan ta kafar dan wasanta mai suna Dybala.
Dybala ya sake jefa kwallo ta biyu cikin minti na 22, Inda daga bisani dan wasan Juventus, mai suna Cheilini, ya saka kwallo ta uku a ragar Barcelona.

A yau kuma za'a cigaba da sauran wasannin inda B Dortmund, zata kara da Monaco, Bayern Munich, zata barje gumi da Real Madrid, ita kuwa Atletico Madrid ta kasar Spain zata fafata da Leicester City, ta Ingila.

Za'a buga wasannin da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi. Wasan da za'a kara tsakanin Bayern Munich da Real Madrid, shine haduwa ta ashirin a tsakaninsu inda a baya suka hadu sau goma sha tara tun haduwar kungiyoyin.

Bayern Munich ta samu nasara akan Real Madrid sau tara ita kuma Real Madrid sau takwas ta samu nasara akan Bayern, anyi kunnen doki sau biyu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG