Bayani Daga Kwararren Malamin Jami'a Kan Auren Zumunci

Tambayar farko da filin samartaka ya yi wa kwararren malamin nan na bangaren sanin halayya da zamatakewar dan adam na jami’ar Bayaro da ke kano, Malam Aminu Danbazau ita ce, me ake nufi da auren zumunci?.

Malamin ya fara da cewar yana mai jan hankalin jama’a da su fahimci cewar, tarihi ya nuna cewa kasashe kansu na samin ci gaba ne ta bangaren yadda suka sami hadin kan juna da kuma zumuntar da ke tsakanin su.

Ya ci gaba da bayyana auren zumunci a matsayin aure ne wanda aka gina shi bisa ga alaka ta jinni, tsakanin dan wa da ‘yar kanwa, ko dan ‘yar kanwa da dan wa ko dan kane.

Ya kara da cewa a bisa al’adar kasar Hausa auren zumunci a shekarun da suka gabata na da matukar muhimmanci domin kuwa a lokacin al’umma bata bunkasa ba, kuma yawanci ba’a cika ba wasu ‘ya’ya su aura ba saboda irin sana’ar su da kuma irin tarihi ko gadon su.

Ga cikakkiyar hirar.