Bayern Munich Ta Yi Wa Porto Mummunan Bugu

Bayern Munich

Robert Lewandowski ya jefa kwallaye biyu jiya talata, a yayin da kungiyar Bayern Munich ta sami kutsawa wasan kusa da na karshe na gasar zakarun turai a cikin shekarA ta 4 a jere inda tayi wa kulob din Porto dukan kawo wuka da ci 6 – 1 a zagaye biyu na wasan da suka buga.

Kungiyar Bayern wadda ke bukatar shafe gibin kwallaye 2 bayan doke ta da ci 3 – 1 da Porto tayi ran laraba da ta shige, ta fito da karfin jiki, ta zura kwallaye har 5 kafin a tafi hutun rabin lokaci, abinda ya kashe gwiwar abokan adawar su tun kafin wasan yayi nisa.

Lewandowski na da kwallaye 22 a duka wasannin, yayin da Thomas Mueller, Jerome Boaten da Thiago Alcantara kuma suka sami nasu kwallayen a zagayen farkon wasan.

Zafin wasan ya ragu ne bayan dawowa hutun rabin lokaci da ya ba kaftin din kungiyar Porto damar jefa kwallo guda.

Porto ta kare wasan da mutane 10 a yayin da aka ba dan tsaron gidan ta Ivan Marcano katin gargadi daf kafin xabi Alonso ya ci bugun free kick, shi kuma koci Julen Lopategui aka koreshi daga filin.P

jefa kwallayen ya kamo kafar sha mafi muni da aka taba yi mata a wasanin cin kofin kulob kulob din zakarun turai a AEK Athens inda ta rasa kwallo 6 – 1 a shekarar 1978.