Bom Ya Tashi A Gurin Bincike Na Sojoji

Ibrahim Ahmed a sansanin 'yan gudun hijira dake Maiduguri

Duk da cewa sojojin Najeriya, na samun nasara wajen kwato garuruwan dake hannun ‘yan kungiyar Boko Haram, amma har yanzu yankunan karkara dake jihar Borno, sun kasance karkashin ‘yan kungiyar Boko Haram.

A jiya ne wasu yara mata ne su biyu suka fito daga jeji, suka nufi wani gurin binciken ababan hawa dake Jakana, sojojin dake gurin basu yarda dasu wadannan yara ba, kwatsam daya daga cikin yaran ta tayar da bom din dake jikinta inda ya halaka ta da kuma wani soja dake kusa da ita, ganin haka sauran sojojin sai suka kwamta kasa kuma suka budewa dayar wuta, inda itama nata bom din ya tashi.

A Shekaran jiya Asabar, wasu yara mata kanana suka fito daga cikin daji akan babura kowannen su tana dauke da bom ajikin ta, akwai wasu da sukaje Ungamdu, wasu kuma suka je Gonari, wadanda suka je Ungamdu su uku tare da wani namiji sunyi kokarin shiga mota alokacin ne bom din daya daga cikin yaran ya tashi, haka yasa direban motar ya tsorata ya gudu kasancewar bai san irin mutanen daya kusa dauka ba. Direban dai ya garzaya ya fada wa jami’an tsaro abinda ya faru.