Manajan Liverpool Brendan Rodgers yace yayi imanin team din sa yayi matukar ganin anfanin hutun da ya samu kafin tafiyar su zuwa Swansea City a ranar litinin.
Brendan Rodgers ya ce “Ina tare da Liverpool, kuma a shirye nake domin in karfafa da tabbatar da wartsakewar ‘yan wasan kafin wasan zakarun Premier League mai zuwa in da Kulob din zai fafata da tsohon kulob din Brendan dake Swansea city a ranar Litinin.
Ta bangaren Mersey kuma, kulob din ya tashi duro ne babu kwallo ko guda a satin da ya gabata, sai dai kulob din na bukatar yin nasara a wasan da zai sake bugawa a Ewood Park, wata mai zuwa kafin ya iya fuskantar Aston Villa a wasan kusa da karshe na wasan zakarun FA.
Liverpool ya buga wasanni uku a tsakanin kwanaki shidda kafin haduwar su Rovers, kuma Rodgers bashi da shakkar cewa irin wannan tsarin mai ban wahala ya addabi kulob din nashi wanda ya gagara a wasannin zakaru 11.