An tabbatar da kungiyar Chelsea a matsayin zakaran gasar wasan turai English Premier League, bayan samin nasarar cinye wasan da suka buga da kungiyar Cystal Place jiya Lahadi inda aka tashi 1 – 0.
Jose Mourinho dai na butakar samun nasara daga cikin wasannin hudun da suka rage a karshe, domin a nada shi zakaran rukunin su bayan samun nasara kan kungiyar Leicester City na ranar Laraba.
‘Dan wasa Eden Hazarda yakara yin rawar gani ga kulub ‘dinsa, inda ya sami nasarar shigar da kwallo ‘daya raga bayan da ya rasa damar cin daga kai sai gola.
Kungiyar Chelsea basu yi wani wasan azo agani ba amma duk da haka sun sami nasarar lashe wasan.
Wannan shine karo na biyar da suka zama zakaran, Mourinho kuwa wannan ya zama karo na takwas da ya samu a rayuwar sa.