Dalibai Mata Sun Daukaka Kara

Dalibai Mata Musulmi a jahar Lagos, sun bukaci kotun dakaka kara da ta shiga tsakani akan hukunci da wata kotu a jahar ta Lagos, ta yanke akan hana mata sanya hijabi a makarantu.

Jaridar Daily Post, ta ruwaito cewa a shekarar 2014, da ta gaba ta mai sharia, G.M. Oyeabo, yayi watsi da wata kara da wasu dalibai mata su biyu Aishat Abdulkareem, da Maryam Oyeniyi, suka shigar inda suka nuna rashin amincewar su da batun hana sanya hijabi.

Shugabanin kwamitin amintattu na kungiyar daliban Musulmi da suka jagoranci daliban da suka shigar da karar a madadin kansu da sauran 'yan uwansu sun ce basu amince da dokar hana sanya hijabi da mataimakin shugaban makarantasu ya bada ba.

Koda yake mai sharia Onyeabo, tayi watsi da karar tana mai cewa dokar hana sanya hijabin bai da wani nasaba da nuna banbanci kuma bai sabawa kundin tsarin milkin Najeriya, na 1999, ba abun da Chief Gani Adetola Kazeem, lauya mai wakiltar daliban ya ce ba gaskiya bane.

Daliban sun bukaci kotun dakaka karar da ta fayace idan hukunci da mai shariar karamin kotun ya yanke na bisan doka ko kuwa a'a.