‘Dalibai Na Amfani Da Twitter Wajen Satar Amsa

WikiLeaks' Twitter page is seen on a computer screen in Singapore. A U.S. court has ordered Twitter to hand over details of the accounts of WikiLeaks and several supporters as part of a criminal investigation into the release of hundreds of thousands of c

Jiya Litinin jami’ar suka ce ana zargin wasu ‘daliban sakandare guda biyu da laifin yin amfani da shafin sadarwa na Twitter wajen satar ansa a jarabawa.

Kamfanin dake hada jarabawar dai yayi hayar wani kamfanin tsaro domin bincikar shafukan sadarwa da suka hada da Twitter, Instagram da Facebook, sun kuma samo lokuta biyu da ‘daliban ‘yan aji biyar na sakandare suka yi satar amsa, inji mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar Maryland.

Amma bai bayyana sunan makarantar da wannan abu ya faru ba, ko sunan ‘daliban da suka yi. Ya kuma ce wannan sabuwar hanyar satar ansa ce suka fito da ita.

An dai samo inda suka copin bayanan jarabawar a shafin sadarwa wanda ya kunshi jarabawar turanci da ake yiwa ‘dalibai a duk fadin jihar, an bincikosu ne sati biyu da suka wuce kuma an dauke su daga kan shafin Twitter.

Duk ‘daliban jiha tar Maryland gundumar Columbia da wasu jahohi goma sha daya, suna sake daukar wannan jarabawa ta kan yanar gizo.

Kamfanin daya kudanar da binciken dai yace, ya samo ire-iren wannan satar ansar inda ‘dalibai ke copan jarabawar a kan yanar gizo, a lokutan da ake baiwa ‘dalibai jarabawar.