Dalilan Da Ke Sa Iyaye Hana Aure -Inji Malama Lami Sumaiya Murtala

Kamar yadda muka ji ra'ayoyin matasa daban daban akan dalilan da ke sa wasu iyaye hana 'ya'yan su auren wasu samari, zaka ga saurayi da budurwa na soyayya kamar yadda ya kamata amma daga karshe sai iyaye su hana.

Ta dalilin haka ne muka ziyarci mala Lami Sumaiya Murtala wadda ta bayyana mana dalilai da dama da ke sa wasu iyaye hana 'ya'yan su yin mu'amular da zata iya kaisu ga aure.

Na farko dai kamar yadda yawancin matasan suka bayyana, iyaye kan gudanar da bincike akan duk wadanda zasu auri 'ya'yan su, dan haka a cewar malamar yawanci idan kaga haka ta faru to lallai iayaen sun hangi wani abu da ka iya cutar da diyar bayan aure, domin masu iya magana sun ce abin da babba ya hando yaro ko ya taka turmi bazai hange shi ba.

A kwai matsaloli da dama da malamar ta bayyana, daga karshe kuma ta bada shawarwari da kuma jan kunen matasa samari da 'yan matadomin kula da kuma gujewa duk wani abin da zai iya kawo masu tangarda a tsakanin su da iyaye da kuma abokan soayyayar su.

Ga cikakkyira hirar.