Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Sirrin Jama'a Ta Kaddamar Da Sabon Kamfe


Wata kungiya mai rajin kare sirrin mutane akan yanar gizo ta kaddamar da wani sabon kamfe domin nuna goyon baya ga kamfanin apple kan takaddamar da yake da hukumomin kasar Amurka domin ya bude hanyar da zasu iya samun bayanan mutane.

Ita dai wannan kungiya da ake kira fight the future na neman magoya baya da suka yarda da kare bayanan mutane akan yanar gizo su yi amfani da # save security a shafukan su na yanar gizo, za a karanta bayanan a bainar jama'a a ranar 22 ga wannan watan a kofar kotun da za'a saurari karar a jahar Califonia ta kasar Amurka.

Wannan kungiya ta shirya wani gangami a watan da ya gabata a yayin da kotu ta umurci kamfanin apple ya bada bayanan sirri dake cikin wayar matashin nan da ya bude wuta a jahar San Bernadinor ta kasar Amurka.

Kamfanoni da kungiyoyi masu yawa sun nuna goyon bayan su ga kamfanin apple jin kadan bayan hukuncin da aka yanke akan fidda bayanan, ciki harda kere keren kayan wuta, da kungiyar kare hakkin dan adam, da cibiyar kare bayanan na'urori.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG