Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Samar Wa Matasa Jari Na Bankin (BOL)


Yau alhamis ne Bankin nan mai suna Bank Of Industry ya kaddamar da wani sabon shiri na kudi Naira bilyan 10 domin tallafawa wajan ba matasa masu shi’awar kasuwanci rancen kudin da zasu ja jari.

Da yake bayani a lokacin bukin kaddamar da shirin a Abuja, ministan dake kula da harkokin masana’antyu Dr Okechukwu Enelamah, ya ce ofishin sa zai hada hannu da dukkan hukumomin gwamnatin kasar domin samar da guraben ayyukan yi,

Ya karada cewa fiye da kashi 40 cikin dari na matasan da ke da ilimin jami’a basa da ayyukan yi kuma kimanin mutane miliyan takwas ne kawai ke samun ayyukan yi a shekara.

Ministan ya bayyana cewa ayyuka da shirin samar da wannan banki na daya daga cikin ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi na sama wa matasa abubuwan yi, inda ya ce shirin zai samar da kusan guraben ayyuka dubu dari uku da sittin a kowace shekara.

Ya yi kira ga wadanda zasu ci moriyar shirin da su yi karfin hali domin biyan bashin da za’a basu akan lokaci domin samun nasarar dorewar shirin.

Mukaddashin shugaban bankin Mr Waheed Olagunju ya kara da cewa duka wadanda ke cin moriyar shirin zasu iya samun kudin da zasu iya kaiwa har Naira miliyan goma da dakika guda na ruwa da zasu biya. A cikin shekaru uku zuwa biyar.

Shugaban ya bayyana cewa wadanda zasu ci moriyar shirin zasu nuna takardar shaidar kammala bautar kasa ta NYSC kokuma ta karatun jami’a, da mutane biyu da zasu tsaya a matsayin shaidu kafin a amince a basu wadannan kudade.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG