Darajar Tsuntsaye Ga Turawa

Kwasakwasa

Kungiyar ceton dabbobi dake jihar California, ta ceto tsuntsuwar kwasakwasa wadda ke da dogon baki kamar Zalbe, a lokacin da aka lura cewa wannan tsuntsuwa ba zata iya tashi ba.

An kai tsuntsuwar zuwa cibiyar ceton dabbobin daji dake birnin Los Angeles, inda ma’aikatan suka tantance cewar ta samu karaya a fuka fukin ta, sun kuma sami kugiyar kamun kifi a kafadar ta, ta dama.

Da farko anyi tsamanin cewa kugiya ce tayi mata wannan rauni, amma bayan da aka ‘dauki hotan x-ray, sai aka ga alamun harsashi daga harbin bindiga.

Likitan dabbobi dai yayi wa wannan tsuntsuwa tiyata da gyara mata fuka fukinta, amma ana cigaba da kula da ita.

Kasancewar haka ne yasa kungiyar dake hankoron kare hakkin tsuntsaye tayi tayin bada tukuicin dala dubu biyar kwatankwacin Naira miliyan daya da dubu dari da hamsim ga duk wanda ya bayar da wani bayani daya kai ga kamo da hukunta wanda ya harbi wannan tsuntsuwa da aka samo a kudancin jihar California.

Kungiyar dai ta fada a jiya Litinin cewa wani ko wata wadda ba’a san ko wanene ba, shine yayi tayin bada tukuicin.