Dokar Hana Shan Sigarin Zamani a Jirgin Sama Zata Fara Aiki

FILE - A smoker exhales vapor from an e-cigarette at the Vapor Spot, in Sacramento, California, in this July 7, 2015, photo.

Masu shan taba sigari dake bukatar dandanon nicotine lokacin da suke cikin jirgin sama da ya tashi daga Amurka ko kuma zuwa Amurka, mai yiwuwa daga watan gobe, za su daina samun wannan damar ta kasancewar za a fara aiwatar da dokar hana amfani da bututun kwalbar da ke aiki da batir don haifar da hayaki na dandanon sigari na zamani.

Ma’aikatar sufuri ta Amurka ta sanar jiya Laraba cewa, an kafa dokar ne domin kare fasinjojin jiragen sama daga shakar hayaki a cikin jirgi lokacin da ake amfani da tabar kwalbar a cikinsa.

An haramtawa fasinjoji shan taba sigari da kuma sauran nau’oin taba a cikin jirgi da dadewa. An ba fasinjojin jirgin sama izinin shiga da tabar kwalba a cikin jirgi, sai dai ba a yarda su dauka a cikin kayan da zasu shigar cikin manyan akwatunansu ba.

An haramta daukar tabar kwalbar a akwati ne bayanda irin wannan tabar tasa wani akwati ya kama wuta. Tabar kwalbar tana amfani da batir ne wanda yake iya kunna kanshi idan ya lalace, ko kuma ya shiga matsi ko wani yanayi na dabam.