Duk Wanda Ya Ja Ruwa Shi Ruwa Ka Duka

Federal Correctional Complex, including the Administrative Maximum Penitentiary or "Supermax" prison, in Florence, Colorado February 21, 2007.

An yankewa wani mutum hukuncin ‘daurin sama da shekaru 28 a gidan yari biyo bayan kaiwa wani maigadin gidan rawa hari, kan rashin jin dadin giyar da aka sayar masa a kulub din.

Mujallar Sacramento Bee ce ta rawaito labarin cewa an yankewa mutumin mai suna Jovan Felix hukuncin ranar juma’ar data gabata, a dalilin harin da suka kai kan wani mai gadin kofa har da caka masa wuka a kofar shiga gidan rawar na garin Sacramento.

Lauya mai gabatar da kara ya bayyana cewa ran Felix ya baci ne akan giyar da aka sayar masa a wannan a gidan rawar, da kuma rashin kulawa mai kyau da yake ganin an nuna masa a ziyarar da yakai wannan kulob, haka ne yayi sanadiyar ‘daura ‘damara da gayyatar abokansa domin komawa kulob ‘din don ‘daukar fansa.

Komawarsu gidan rawar ne suka rufarwa maigadin kofa da duka harma da caka masa wuka.

Alkalin da ya yankewa wadanda ake tuhuma hukunci mai suna Robert Twiss, ya yi Allah wadai da aikin suka aikata, yakuma yanke musu hukunci mai tsanani.