Babban mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Seyi Akinwunmi, ya tabbatar da cewa kwach na kungiyar kwallon kafar samari ‘yan kasa da shekara 17 ta kasar, Golden Eaglets, watau Emmanuel Amuneke, zai ci gaba da rike mukaminsa.
Amuneke ya jagoranci ‘yan Eaglets wajen samun nasarar kare kofin na duniya bana a gasar da aka yi a kasar Chile cikin wannan watan.
A wajen wata liyafar cin abincin daren da aka shirya ma ‘yan wasa da jami’an da suka jagorance su, Akinwunmi yace hukumar ta NFF ta yarda cewa Amuneke zai ci gaba da zama kan wannan mukami domin renon sabbin ‘yan Golden Eaglets da za a dauka, wadanda kuma a shekara mai zuwa zasu fara shirin gasar cin kofin Afirka da na duniya na shekarar 2017.
A lokacin da yake bayyana dalilin haka kuma, Akinwunmi yace hukumar tana so ne ta kyale masu koyar da wasanni na kowane matsayi su saba da tsarin matsayinsu tare da yin aiki da juna sosai ta yadda mai koyarwa na yara na iya sauya matsayi zuwa mai koyar da manya cikin sauki. Yace babban abinda suke son yi shi ne karfafa bunkasar wasan kwallon kafa na matasa.