Fada ya Barke Tsakanin Bangarorin Matasa Biyu

Wasu matasa kenan

kazami fada ya barke tsakanin bangarorin matasa biyu a unguwar Oshodi, a birnin Lagos, sanadiyar karbar kudaden lodin motoci a garejin dake Oshodi.

Ricikin dai yayi sanadiyar mutuwar mutun daya, wadanda a lokacin da kowane bangare na masu karbar kudaden lodi, ya ja dagar cewa shine ke da hakkin karbar kudi a wajen masu lodin motoci dake zirga-zirga zuwa wasu sassan da wajen birnin Lagos.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Lagos, ya kai ziyara, a tashar motar ta Oshodi, don ganewa idonsa, da kuma jibge jami’an ‘yan sanda don tabbatar da doka da oda.

Wadannan Matasa da suka yi bata kasha suyi amfani da makamai irin su adduna da bindigogi da dai sauransu.