Bayan lashe kofin gasar matasan Afrika na ‘yan kasa da shekaru 20 da Flying Eagles ta yi a Senegal, mai horar da ‘yan wasan Najeriya Manu Garba, ya ce ‘yan wasan nasa za su iya zama manyan ‘yan wasan kasar a nan gaba.
A cewar Garba, wanda ya nuna matukar farin cikinsa a fili, samo ‘yan wasa daga makarantun horarwa, su kuma lashe kofin gasa kamar wannan, alama ce da ke nuna cewa harkar kwallon kafa na bunkasa a Najeriya.
Manu Garba ya ce yana mai cike da farin cikin lashe wannan kofi domin shi ma yana daya dag cikin ‘yan wasan Najeriya da suka lashe kofin wannan gasa a shekarar 1983.
Hakan na nufin mai horar da ‘yan wasan ya lashe kofin a matsayin dan wasa da kuma matsayin mai horarwa.
Kwallon da dan wasan Najeriya Bernard Bulbwa ya zira a ragar Senegal kafin a je hutun rabin lokaci ne ta baiwa Najeriya damar lashe wasan karshe da ci 1-0.
Yanzu haka Najeriya ta na rukuni daya da Brazil da Hungary da Korea a gasar kwallon kafa ta matasa da za a buga New Zealand.