Hattara Dai Matasa

Wani matashi mai shekaru 36 da haihuwa ya amsa laifin da wata kotu ta tuhumeshi na aikata fashi da makami a wani banki dake jahar Pennsylvania ta kasar Amurka ta wajan yin amfani da bam din karya.

Kotun ta tuhume shi da laifukan da suka hada da yin bazarana da tada hankalin jama'a, da fashi da makami duk da shike bam din ba na gaskiya bane amma a cewar alkalin, matashin ya yiwa jama'ar barazar hallaka su a cikin harabar bankin.

Kamar yadda alkalin ya bayyana, matashin ya ce yayi amfani da wayar hannu da kuma hada wayoyi da sauran wasu dabaru ne domin abin yayi kama da bam, kuma dalilin da yasa yayi haka shine akwai wasu kudi da ya tara har dalar Amurka dubu tara domin tafiya yawon shakatawa da zarar an kamma daura masa aure amma sai aka wayi gari kudin sun kare tun kafin lokacin.

Ta dalilin haka ne matashin ya jefa kansa a cikin wannan muguwar hanya wadda daga karshe ya tsinci kansa a yanayin da yake ciki a yanzu