Hattara Matasa! Kungiyar Boko Haram Ta Bude Sabuwar Tashar Radiyo

Har yanzu tsugunu bata kare ba, domin kuwa rahotanni daga jamhuriyar Kamaru sun bayyana cewa maharam boko haram sun bude wata sabuwar tashar radio ta FM a garin tolkomari kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru inda suke watsa shirye-shiryen su na kalubalantar kasashen da suke ikirarin chin galaba akan su FM din na da frequency meter 96.8 MHZ a tolkomari a jihar arewa mai nisa.

Wannan gidan Radiyo dai kamar yadda rahotanni suka bayyana, yana kafe ne a wani kauye dake kan iyaka Tsakani Najeriya da jamhuriyar Kamaru wanda ake kira Talkomari. Jama’ar wanna kauye sun ce suna jin yadda wannan gidan Radiyo ke yada shirye shiryen sa.

A wata hira da wani mazaunin kauyen wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa da zarar gwamnatin Kamaru ta bayyana samun galaba akan ‘ya’yan kungiyar sai suma su fito ko su karyata lamarin kokuma suma su fadi irin tasu nasarar da suka samu, da kuma kara fadawa jama’a cewar suna nan daram babu abinda ya same su.

Malamin ya kara da cewa jama’a da dama sun tabbatar da jin wannan gidan radiyo sai dai kamar yadda ya bayyana, har yanzu ba’a gano taka mai-mai inda dakin yada labarum yake ba.

Wannan lamari na ciwa gwamnatin Kasar tuwo a kwarya a kokarin ta na gano taka mai-mai inda wannan dakin yada labaru yake.

Ga rahoton Garba Auwal daga jamhuriyar Kamaru.