A harkokin fasaha na wannan zamani mata ba’a barsu baya ba, idan aka duba kan yanar gizo musammam shafikan sadarwa na zamani da suka hada da Facebook, twitter da Instagram, za’a ga duk mata na amfani dasu.
Matsala anan shine duk inda matan Hausawa ke zuwa akan hanyoyin sadarwa na zamani ba guri bane da zasu nemi ilimi, guri ne da zasu nuna kansu – inji Mohammed Hashim wani masanin na’ura mai kwakwalwa, yakuma nemi matan Hausawa dasu rika tashi domin neman ilimi kamar yadda sauran kasashe da suka cigaba a duniya sukeyi.
Shirye shiryen na da kai na iya taimakawa kwarai da gaske wajen fahimtar da mata domin su dukufa wajen neman ilimin fasaha na zamani. Kafa kungiyoyi da zasu rika taimakawa wajen ilimintar da matasa maza da mata da samar musu hanyar zuwa makaranta da taimako, hakan zai taimaka kwarai da gaske ga karin ilimin fasaha ga mata.