Illar Shafe Shafe Dan Samari Da Gargadi Ga Masu son Farar Mace Ko da Mayya ce

Cikin tattaunawar wannan makon, Dr Shehu na asibitin malam aminu Kano ya yi mana cikakken bayani dangane da irin illar da shafe shafe da wasu ‘yan mata ke yi domin canza launin fatar jikin su a sakamakon sanin cewa samarin wannan zamani sun fi son farar mace.

Da farko likitan ya bayyana irin rashin lafiyar da waddannan kayan shafe shafe ka iya haifarwa domin jinni yakan debe su ya kai su wurare daban daban a cikin jikin dana dam. Bauan haka akwai cututtuka wadan da suka hada da fitowar kuraje da zarar an bar anfani da irin wadannan man shafawa, yana iya kawo hakiya, ko hawan jinni na ido ko nankarwa da sauran su.

Ya kara da cewa fatar mai shafa irin wannan man shafawa bata da karko, kuma idan mai ita ya ji rauni, yakan dauki lokaci bai warke ba, da kuma saurann matsaloli makamantan su.

Daga karshe sai jawabi daga bakin Malama Lami Sumayya ta yi kyakkyawan bayani akan irin illar da samari ka iya fuskanta a sakamakon kwadayin auren farar mace.

Samari dai na cewa sai farar mace koda mayya ce, to amma ba nan take ba inji malama Sumayya, domin kuwa iadan saurayi ya matsa dole sai farar mace to yana iya aurowa kanshi ruwan dahuwar kansa.

Masu iya magan sun ce tsun tsun da ya kira ruwa shi ruwa zai ba kashi.

Ga cikakken Shiri.