INEC A Shirye Take Da Babban Zabe Mai Zuwa

INEC

Hukumar zabe a Najeriya ta ce ko a yau aka ce a gudanar da zabe, ta kammala dukkan shirin da ya kamata ta yi. A hirarsu da Ibrahim Alfa Ahmed, mataimakin darektan yada labarai na hukumar ta INEC, Nick Dazan, yace a yanzu haka kayan zabe na jihohi, kuma jibi laraba zasu isa dukkan kananan hukumomi.

Mataimakin yada labarai na hukumar INEC, yace a yanzu haka sun rarraba katinan zabe na din din din kashi tamanin da biyu bisa ‘dari ga ‘yan Najeriya, an kuma yi wa mutane rijistar karshe tsakanin Juma’a data wuce zuwa ranar Lahadi, mutanen da ba’a buga katinan su ba kimanin mutane dubu ‘daya, suma an samu nasarar rabawa yawancin su katinan.

A game da kayan aikin zabe na sirri wanda suka hada da akwatunan zabe, takardun kada kuri’a, da kuma takardun tubuta sakamakon zabe duk yanzu haka suna ajiye a bankin tarayya a jihohi, kuma za’a rarraba kayan ne agaban ‘yan takara ko wakilansu. Ranar jajiberan zabe Juma’a za’a kai kayayyakin gundumomin zabe kimanin dubu tara na kananan hukumomi.