Jami’an tsaro sun dukufa wajen wayar wa da jama’a kai wajen matakan da zasu rika dauka a yayin da aka samu fashewar bom.
Ganin yadda hare-hare bom ke sanadin dinbin rayuka, hukumomi sun fara gayawa jama’a matakan da zasu rika dauka don tserar da rayukansu.
A cewar jami’I mai kula da sashen warware boma bomai na rundunar ‘yan sandan jihar Plato, DSP Abel Mbibi, yace, yana da wuya mutane su tantance bom, sai dai in sunyi la’akari da wani abun da ba kasafai suke gani a muhallinsu ba, sai suyi nesa da shi su kuma nemi taimakon jami’an tsaro. DSP ya kara da cewa, “shawarar da muke bawa jama’a na farko shine, a rika gudanar da bincike da na’ura dake iya gane abu mai hatsari a jikin mutum, kuma kamata yayi a rika gudanar da binciken duk wani mutum mai shiga kowacce haraba daga waje, ko mutum a kafa yake ko a abin hawa.
Alokacin da bom ya tashi, me jama’a yakamata suyi? Tambayar da wakiliyar mu Zainab Babaji, ta yiwa sufeton ‘yan sanda Ezekiel Tali, shi kuma yace, “in bom ya riga ya tashi, indai bai tabaka ba kar kayi saurin guduwa ko ina, kayi kokarin kwantawa a kasa, zai iya zamantowa akwai wani zai iya kara tashi.
Sufeto Ezekiel, dai yayi kira ga mutane da su guji saurin zuwa inda bom ya tashi domin kallo ko daukar hotuna, domin baza’a taba sani ba, zai iya yiwuwa akai wani bom an dasa kuma zai iya tashi yakuma illata mutane da yawa fiye dana farko.
Fadakarwar ta ‘yan sandan dai na zuwa ne alokacin da gwamnatin tarayya ta fito da wasu bayanai data bankado wanda kenunin cewa ‘yan ta’adda a Najeriya, na shirin kai hare-hare da amfani da matasa maza da dabbobi kamar su Awaki, Shanu, da Rakuma. A cewar sanarwar maharan sun kuduri kai hare haren a kasuwanni, wuraren cin abinci, wurin na’urar cirar kudi ta ATM, da taron gangamin siyasa harma da wajajen ibada, sanarwar ta kuma gargadi jama’a da su gujewa cincirindon jama’a, sukama kula da duk wani take taken da basu yarda da suba.
Your browser doesn’t support HTML5