Tsohon Darektan Hukumar Wasanni ta NSC, Patrick Ekeji, ya ba da shawarar cewa kada a baiwa ‘yan wasan Golden Eaglets lambar grimamawa ta kasa, bayan kofin da suka lashe a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17.
A cewar Ekeji, wanda shima tsohon dan wasan Najeriya ne kuma tsohon koci, kamata ya yi a saka su a turbar da za su kwaikwayon na gaba da su, domin ta haka ne kawai za a iya taimakawa ‘yan wasan.
Ekeji ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Owerri a jiya Talata, yana mai nuna damuwarsa kan makomar ‘yan wasan bayan da suka lashe kofin duniya a wannan shekara a Chile.
‘Yan wasan na Eaglet sun lashe kofin ne a karo na biyar inda a wannan jiko suka kare kofin wanda dama yana hanunsu.
Ya kara da cewa dama maksudin shirya wannan gasa shi ne a hada kan matasa domin su nuna bajintarsu.