Kaji Yadda Ake Cewa A Garin Wasu

Bana Bakwai

Adamu Aliyu daga jihar Filatu cewa yayi Sabuwar Kalma da matasa ke fada idan ka ji mutum na cewa ‘kowa ya ji bari ya ji hoho wato misali ga masu harkar kasuwancin idan wani ya zo sayen kaya a wajen makwabcinka sai ka ga wanda ya zo sayen kayan ya taba sayan kayan ka kuma baya biyan bashi a kan lokaci to sai ka ce wa kowa ya ji bari ya ji hoho dan mutum sai mutum

Shi kuwa Abdullahi soron dinki daga Kanon Dabo cewa yayi a wajen su idan aka ce wannan jakwal ne ana nufin abu mara kyau ko budurwar da bata hadu ba ko ma water wayar hannu da ta tsufa ta kuma fita daga yayi .

Baya ga haka kuma Kalmar “ya dau jarka” misali idan dan adaidaita sahu ya dauki dan unguwarsu ko wani wanda ya sani to sai a ce ya dau jarka domin kuwa ba biyan kudi zai yi ba.

Har ila yau akwai Kalmar “ya taka kwado” tana nufin idan mutum na da abin hawa sai yayi faci sai a ce ya taka kwado

A biyo mu domin jin shirin mu na bana bakwai a dandalin voa, ku kuma rubuto mana lambobin wayar ku domin jin irin naku salon maganar.