A kwanakin baya ne dai ‘yan sandan kasar Mexico suka kamo wata yarinya a makaranta da ake tsammanin tayi gudun gida, har ma aka ‘dauke ta zuwa Amurka gurin wata mata da ake tsammanin itace mahaifiyar ta.
An dai kame yarinyar mai suna Alondra Luna Nunez ne da kai ta gurin iyeyen da ba nata ba a rashin sani, hakan kuwa ta farune alokacin da jami’an Amurka su gayawa takwarorin su na Mexico cewa, matar ta tabbatar musu da cewa ta san inda ‘yar ta take bayan ta ‘bace shekaru bakwai.
‘yan sandan mexico dai sun kamo yarinyar batare da gudanar da bincike ba, hotan bidiyon kama yarinyar a lokacin da take makaranta ya bazama kan yanar gizo inda mutane dayawa ke magana kan gaskiyar lamarin. Hakan ne yasa aka gudanar da gwajin da ake kira DNA, domin tabbatar da cewa itace yarinyar ko ba ita bace, daga karshe dai sakamakon DNA ya nuna cewa wannan matar ba ita bace mahaifiyar Alondra ba.
An kuma dawo da yarinyar kasar Mexico gurin iyayenta, alokacin da taron ‘yan jarida ke kokarin yi mata tambaya bayan saukar ta daga jirgi tace, “ku tambayeni komai kuke so gobe, yanzu haka ina son na kasance da iyaye na ne kawai.”