Kamfanin Microsoft Zai Sallami Ma'aikata 1,850

Kamfanin Microsoft ya fitar da wata sanarwa cewar zai sallami ma’aikatan kamfanin guda 1,850 da kuma kai karshen cigaba da kasuwancin kera kayan wayar hannu da kamfanin yake tsakanin sa da kamfanin Nokia.

A yau laraba ne sanarwar ta fito inda kamfanin ya bayyana shirin da yake na sadaukar da guraben ayyuka 1,850 a dalilin daina cigaba da wannan kasuwanci kuma hakan zai dakatar da guraben ayyuka 1,350 a kasar Finland inda kamfanin yake tsarawa da kera wayoyin hannun. da kuma sauran a wasu wurare.

Babban manajan kamfanin dake kasar Finland Mr Kalle Kiil ya bayyana cewa sauye sauyen da kamfanin zai yi, zai yi asarar zunzurutun kudi kusan dalar Amurka miliyan 950, na kamfanin.

Wannan yanan nufin cewar kamfanin na yunkurin kakkabe sauran barbashin kayan aikin kamfanin wayar Nokiya wanda yayi fice a wajan kera wayar hannu a duniya daga shekarar 1998 zuwa shekarar 2011 da farin jinin wayar yayi kasa warwas.