Katafaren Jirgin Ruwan Kasar Koriya Ya Yi Batan Dabo

Wani babban jirgin ruwan Koriya Ta Kudu na dakon kaya, wanda ke dauke da mutane 24, ya bace a tekun Atlantika, bayan tuntubarsa ta karshe da jami'ai daga tazarar kilomita 2,500 daga gabar Uruguay.

Kafar labaran Koriya ta Arewa ta Yonhab, ta ce rabon a ji duriyar jirgin ruwan mai suna Stellar Daisy, mai nauyin ton 266,000 tun ranar Jumma'a, lokacin da wani daga cikin matuka jirgin ya aike da sako cewa jirgin na fuskantar barazanar nitsewa. Ranar 26 ga watan Maris jirgin ya bar Brazil.

"Al'amari ne mai bukatar daukin gaggawa," a cewar takaitaccen sakon, wanda ya kara da cewa, "Ruwa na yoyo a sashi na biyu."

Daga bisani kuma kafar ta Yonhab, ta ce an samo biyu daga cikin matuka jirgin su na iyo bisa ruwa kuma an ceto su. To amma ya ce an samu wasu kwale-kwalen ayyukan ceto a wurin babu komai ciki.