Ko Kanada Magajin Da Zai Gaji Shafin Facebook Dinka?

mutane na shiga shafin facebook ta kan wayoyin su.

Shafin sadarwa na Facebook ya fara baiwa mutane dama da zasu zabi magaji bayan da rai yayi halinsa, inda duk wanda aka zaba zai cigaba da kula da shafin.

A baya idan Allah ya dauki ran mutum, ‘yan uwan sa ko abokansa sai dai su tuntubi kamfanin Facebook domin rufe shafin, ko kuma a maida shafin ya zamanto na shafin tunawa da mutum.

Amma a yanzu idan har mutum ya zabi magaji, to magajin nan na da damar bayyana mutuwar ka, harma da bayar da bayanan jana’iza domin duk abokanka na shafin Facebook su sani. Kamfanin Facebook dai yace ‘yan uwan mutanen da suka rasa rayukansu da dama na tuntubar kamfanin domin ganin an basu damar shiga shafin su canza hotuna ko kuma rufe shafin har abada. Amma yanzu da wannan dama da mutun zai iya zabar wanda ya yarda dashi ya kula masa da shafin ko bayan ransa zai kawar da wanan matsala.

Mutane na iya shiga cikin shafin sadarwar su domin ganewa idanuwansu yadda ake zabar wannan dama, shiga setting sai a danna security za’a ga legacy contact.