Ku Kama Sana'a Mata - Inji Malama Hadiza Abdullahi

A kamar yadda muka saba zantawa da mata daban daban domin jin ta bakinsu musamman kan yadda ake damawa da su a ayyukan yau da kullum, yau dandalinvoa ya sami zantawa da wata mata mai suna Hadiza Abdullahi wadda ta shafe shekaru goma tana sayar da kayan mata da suka hadar da sutura da kayan miya.

Matar Ta ce da sana’ar ta, har fili ta samu ta saya duk da cewa tana da yara da kuma sauran abubuwan rayuwa da take kula da su amma hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba.

Malamar ta yi kira ga sauran mata da su mike domin nemnan nakan su, kuma ta kara da cewa dogaro da kai yana da matukar alfanu duk da cewa mazan su ke daukar yawancin dawainiyar iyali, hakan zai taimaka wajan magance wasu matsalolin.