Kwastam-Duk Wanda Aka Kama Da laifin Cin Hanci Zai Sha Daurin Shekaru 10

Tamerlan Eskerkhanov, Shagid Gubashev and Ramzan Bakhayev (L to R), detained over the killing of Boris Nemtsov

Shugaban hukumar kwastam na kasa mai ritaya Col Hameed Ali ya ja kunnen jami'an hukumar ranar talata da ta gabata da cewar duk ma'aikacin hukumar da aka kama da laifin cin hanci da rashwa, lallai za a gurfanar da shi gaban kuliya kuma za'a yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan kaso.

Shugaban ya yi gargadinne a jahar Sokoto yayin da yayi wa ma'aikatan na kwastan jawabi a jahar.

Shugaban ya kara da cewa ya kamata duk jami'in da ya shiga aikin ya zamanto ya shiga ne domin bautawa kasar sa da gaskiya ba neman azirta kansa da haramtacciyar hanya ba.

Ya ce bawai yana nufin babu lalatattu a hukumar bane, dole ne akwai su amma su kuka da kansu.

Daga karshe ya yi kira ga jami'an da su kasance biyayya da bin doka, da kuma kiyaye ka'idojin aikin su.