Mai Ke Jan Hankalin 'Yan Mata Su Rika Sa Matsattsun Wanduna?

Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, shirin samartaka na kawo maku ra’ayoyin matasa maza da mata akan batutuwa da dama da suka shafi rayuwa da zamantakewar matasa a wurare daban daban.

A wannan makon mun tattauna ne akan yadda wasu ‘yan mata suka rungumi dabi’ar sa dogon wando kuma mai kama masu jiki wanda aka fi sani da Legins a turance, har ma su fita cikin al’uma ba tare da jin kunya ko nauyin irin kallon da jama’a zasu yi masu ba.

Koda shike ba’a taru an zamam day aba kamar yadda wasu daga cikin wadanda muka ji ra’ayoyin su suka bayyana, wasu na sa wando ne domin su burge abokan soyayyar su kosauran jama’a,. Haka kuma wasu na sawa ne ne domin yafi sauki fiye da zane ko sikyat da aka san su da shi a cewar su.

Tambayar anan ita ce, mai ke jan hankali ko ra;ayin yawancin ‘yan mata har su kai ga amfani da irin wannan sutura baya ga wadda aka san su da ita a matsayin sun a mata?

Samari da dama sun bayyana cewa a nasu tunanin neman a yabe su ne da kuma kwadayin al’adun wasu da kuma daukar zuga daga takwarorin su maza, sun kara da cewa idan budurwa ta sa kaya koda kuwa kayan basu yi mata kyau ba idan saurayinta ya ce tayi kyau haka zata dauka kuma kullum zata so mai maita hakan domin a ganinta ta burga.

Daga karshe kamar yadda wasu suka ce, zamani ne ya canza kuma a ganin su tafiya dai dai da zamani ba laifi bane.

Saurari cikakkiya kirar.