Kamfani Apple zai fitar da wasu sabbin kayayyakinsa a ranar Ashirin ga wannan watan, kwana guda kenan kafin Apple ya bayyana gaban kotu don kare kan sa daga bukatar gwamnatin Amurka na ya taimaka ya bude wata wayar iphone dake kulle.
Manazarta da masu rubuce rubucen fasaha su na sa ran Apple zai gabatar da sabuwar wayar iphone mai girman inci 4, da wata karamar na’urar ipad pro har ma da wani sabon agagon Apple. Amma kamfanin bai bada wani karin haske kan kayayyakin da zai gabatar ba, hakan ya dace da yadda kamfanin ya saba yi wajen janyo hankali jama’a da dokin su ga sabbin kayayyakin da zai gabatar..
An aikawa manema labarai gaiyata jiya Alhamis, wadda ke cewa “ ana son a gaiyace su cikin” Hedikwatar Apple na jihar California a Amurka.
Bikin kaddamar da sabbin kayayyaki da kamfanin Apple yake yi sau biyu a shekara, yana janyo yadda jita jita da kuma dokin jama’a. Bikin wannan shekarar dai yazo ne a lokacin da kamfanin ke cikin jayayya da hukumar binciken aikata laifuffuka ta FBI da gwamnatin Amurka, yayinda suke kokarin takurawa kamfanin kan manhajar da yake amfani wajen kare bayanan masu amfani da wayoyin iphone.