Sarakunan gargajiya a jihar Nasarawa, suna cigaba da gargadin matasa akan su tabbatar basu yadda wasu sunyi amfani dasu wajen hada rikici yayin gudanar da zabubbuka ba.
A cewar mai martaba sarkin Kwandare a jihar Nasarawa, da aka ba sandar girma zuwa sarki mai daraja na daya Alhaji Ahmadu Alma Kura, jama’a su tabbatar sun karbi katin zabensu, sukama yi zabe bisa cancanta, inda yace, “Mu muna rokon dukkan jama’ar Najeriya, duk cikakken mutum daya kai shekara goma sha takwas to don Allah don Annabi, yaje ya karbi katin zaben shi don ya kuma san makamin sa na hannunsa.” Ya kuma cigaba da cewa a cikin wannan al’umar babu wani sarki daya zauna domin ya huta, kowa yana son ayi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma ko wacce juma’a idan aka taso daga masallacin juma’a muna kiran talakawa da babban murya da zu jajirce su tsaya ayi zaben nan lami lafiya.
To sai dai har yanzu wasu jama’a na korafin rashin samun katin zaben, kamar yadda wasu mutane dayawa suka shaida wa wakiliyar mu Zainab Babaji, cewar har yanzu dai basu sami katinan zaben suba. Amma jami’in hulda da jama’a na hukumar zabe mai zaman kanta Abubakar Aliyu Mohammad, ya shaidawa wakilayar tamu cewa har yanzu ana cigaba da raba katunan zabe ga mutane, idan kuma mutum har yanzu bai karbi katin zaben sa ba to ya garzaya ofishin karamar hukuma na hukumar zabe mai zaman kanta domin a karbi katin.
Your browser doesn’t support HTML5