Maza Ma Ba A Bar Su A Baya Ba A Gangamin Abuja - 30/4/2014

Shugaban Majalisar Dattawa David Mark da Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal suna yi wa Mata jawabi a kofar Majalisa a cikin ruwan sama.

Maza ma sun yi cincirindo a wurin gangamin da dubban mata suka yi yau laraba a Abuja domin nuna bacin rai da alhinin sace dalibai mata da aka yi daga makarantar sakandare ta garin Chibok a Jihar Borno, kuma har yanzu ba a kwato su ba.

Dr. Jibrin Ibrahim,w anda ya halarci wannan taron shi ma, yace ya je ne a matsayuinsa na uba, domin shi ma ya nuna damuwarsa kan wannan al'amari, tare da neman lallai hukumomi su san yadda zasu kwato wadannan yara daga hannun 'yan ta'adda.

Your browser doesn’t support HTML5

Dr. Jibrin Ibrahim A Wurin Gangami Na Abuja: Mu Ma Iyaye Ne - 0'43"